Me ka ke nema?


Shafin Farko

‘Yancin Rayuwa Ghana


Kundin Tsarin Mulkin Ghana
Hoto: Office Holidays


Gabatarwa

Matashiya:
Dukkan abin da za a karanta daga wannan gaɓa zuwa ƙarshen wannan shafi, fassara ce kai tsaye daga Kundin Tsarin Mulkin Ghana na shekarar 1996 wanda aka ɗauke a shekarar 2021 daga shafin: https://constitutionnet.org

Sashe na 13: Kariya ga ‘Yancin Rayuwa

Wannan sashe ya zayyana waɗannan tanade-tanade a matsayin 'yancin duk wani ɗan Ƙasar Ghana ta fuskacin rayuwa.

  1. Babu wani mutum da za a raba shi da ransa haka kurum saidai a yanayi na zartar da hukuncin kotu cikin abin da ya shafi manyan laifuffuka a ƙarƙashin dokokin Ƙasar Ghana wanda aka yanke masa hukunci.
  2. Mutum ba za a tuhume shi da laifin hana wani rayuwarsa ba bisa tanadi na (1) na wannan sashe idan har wancan mutumin ya mutu a sakamakon halastaccen yaƙi ko kuma wancan ɗaya mutumin ya mutu a sakamakon amfani da ƙarfi bisa gwargwadon yadda za a iya tabbatar da gaskiyar hakan a takamaiman yanayi:
    1. bisa dalilin kare kowane mutum ne daga ruɗanin-rikici ko a dalilin kare dukiya; ko
    2. domin a aiwatar da halastacciyar tsarewa ko a hana kuɓucewar mutumin da ake tsare da shi bisa doka; ko
    3. bisa dalilan kwantar da tarzoma, bore ko tawaye; ko
    4. bisa yunƙurin kare hukumar kula da laifuffuka (commission of crime) daga wannan mutumin.


Shafin Tarihi
Shafin Ghana
Ƙabilun Ghana
Yankuna Ghana

Shugabannin Ƙasa


Tarihin Ghana

Haƙƙoƙin 'Yanƙasa

‘Yanƙasanci
Haƙƙoƙi da ‘Yanci
‘Yancin Rayuwa
'Yancin Walwala
Girmama Ɗan'adam
Kariya Daga Bauta
Yancin Daidaito
Kaɗaikatar Gida
Adalcin Shari’a
Kariya Daga Ƙwace
Muhimman ‘Yanci

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub